Wakar Mallam Bello - Michigan State University

Wakar Mallam Bello

Creator: Kwamso Laouali Performer: Naoul? dan Jagga

Na an mai gundumar mutanen Yardaje. Alkawali ya cika. Na Kamsila Awwali Abdou alkawali dai ya cika. Waa ta mutanen na Lawiza (Malam Bello). Alkawali dai ya cika. Na Malam Haruna komi ya yi daidai. Na Malam Mansur wanna alkawali da ka dauka na mutanen Kano. Ka auki alkawalin mutanen Zango. Ka auki alkawalin mutanen Yardaje.

Daga nan sai ka taho. Ka auki alkawalin mutanen Tumfafi da na Kokai. Ka auki alkawalin mutanen yi kuwa Kufai da Hamada mai aiki da gaskiya baban

Usmaila. Sai ka taho ka auki alkawalin mutanen. an Badada da na Kwari, duka wannan aiki ne da gaskiya a gurin Malam Bello na Lawiza

sarkin aiki. Ga amarya da ango sun zo sai a yi musu waar aure. Ga amarya da ango sun zo sai a yi musu waar aure. Sai hura ta taka, Zuwaira ma ta taka mai ganga ya doka don mu yi musu waar

aure. Zango local gamen Daura local gamen sun biya mu ta kowane hali. Mu gaida Habibu angon Ladi shi ma ya zo waar aure. Ga amarya da ango sun zo sai mu yi musu waar aure. Sai mu gaida Salisu Lauya shi ma ya zo waar aure. Idon Mota an kira mun gaishe shi angon Mari ya mana komi. Ga amarya da ango sun zo sai mu yi musu waar aure. Sarkin aiki Malam Bello shi ma ya zo waar aure. Ga amarya da ango sun zo sai mu yi musu waar aure. Na Lawiza Malam Bello ya biya mu ta waar aure. Baon Kano mun gaishe shi ya biya mu ta waar aure. Malam Bello baon mutanen Yardaje shi ma ya zo waar aure. Malam Bello baon yi kuwa Kufai da Hamada ya biya mu ta waar aure. Baon Kwari da an Badada shi ma ya zo waar aure.

Ga amarya da ango sun zo sai mu yi musu waar aure. Da ka je birni ka lalace har gara ka zauna auyenku. Bismillahi za mu farawa da waan ungiyarmu. Na Allah ba ya arewa na Annabi ba ya arewa waar ungiyarmu wadda manya sunka tsara ta. Li'ilafi kore shi a niyar kowa ta bi shi don mu yi ta ma yi ta arziki ce. Baki ya ci kanshi mugu. Malam Bello za mu gaida shi, shi ma ya ba mu hairan. Angon Lawiza za mu gaida shi ma ya ba mu hairan. Malam Bello baban Usmaila za mu gaida shi ma ya ba mu hairan. Mansur an Bello za mu gaida shi ma ya ba mu hairan. Yardaje za mu koma su ma sun ba mu hairan. Anwali Abdou za mu gaida shi ma ya ba mu hairan. Yi za mu yi ba mu fasawa an mata sun biya mu, samari ma sun biya mu ji dain

rayuwarmu. Sarkin aiki za mu gaida na Lawiza ya biya mu, Malam Bello mun gode hairan. Soyayya, soyayya wasa ba faa ba. Mu gaida Salisu Lauya shi ma ya biya mu. Mu gaida Idon Mota an kira shi ma ya biya mu, angon Mari ba mu rena kyauta. Ina san ira? Ya ba mu domin so da yarda. an mata mu rausaya domin gaida Nura. Ina Nura na Aisha? Mun gode da kyauta.

Usman mun gode da kyauta. Mu gaida Malam Bello shi ma mun gode da kyauta. Na Lawiza Baban Ariel mun gode da kyauta. Baban Usmaila mun gode da kyauta. Na Lawiza sarkin aiki. Yau ne ranar aurin auren Malam Haruna da amarya Nana Tsaiyaba. El Haji Malam Haruna na Tsaiyaba mi Allah, zankon dutsi ka fi gaban Askewa, Tureka sai

da gaban ikon Allah. Na mai gari Aminu na mai gari Sule na Malam Suli Dari Dauda ruwa maganin daua, na

Suli Jaga mutuman Jaga mi masaukar bai. Malam Bello na Lawiza, sarkin aiki, sabo da kai Malam Bello aka ba ni ni an ira naira

ashirin. Malam Bello sarkin aiki an ba ni kui sabo da kai na Lawiza sarkin aiki. Allahu akbar! Ina kyanwa? Na Lawiza a gaya mana Lawiza sarkin aiki ranar da ka rufe

Lawiza a aki ran nan ka ata mana rai, ranmu ya aci. Ba mu ji ba dai. Ka yi wa Alhaji Malam Haruna laifi. Ni ma an kira ban so ba raina ya aci. Ba mu ji dai

ba. Ka yi wa Alhaji Malam Haruna laifi. Ni ma an kira ban so ba raina ya aci. Sabo da kai Malam Bello, Malam Lawan mi alibai ya ba ni naira ashirin ni an kira Idon Mota na gode. Godiya nike. Mu gaida Mansur an Bello ya ba mu domin so da yarda. Na Malam Bello ya ba mu domin so da yarda. Na Lawiza sarkin aiki ya ba mu domin so da yarda. Uban Usmaila ya ba mu domin so da yarda. Uban Ariel ya ba mu domin so da yarda. Angon Lawiza ya ba mu domin so da yarda. Mu taka rawarshi ko kwa ba mu da lafiya ne? Mu gaida Kamsilo Awali Abdou ya ba mu domin so da yarda. Mu gaida amarya da ango, ina Malam Haruna na tsaya ba? Mun gode da kyauta

alkawalin amarya da ango ya cika. Ina Malam Haruna na Tsaiyaba? Mun gode da kyauta. Karayarku ma Hassada ta Allah ba taku ba. Ina Malam Bello na Lawiza? Mun gode da kyauta. Malam Bello na Lawiza mun gode da kyauta. Baban Usmaila na Lawiza mun gode da kyauta. Soyayya, soyayya wasa ba faa ba. Baban Ariel Bello shi ma ga mu gaida. Sarkin aiki na Lawiza mun gode da kyauta. Sai ko mu durusa gaba aya domin ziyara gaban manya su yi mana kashe kowa ya gani, to mun gode. Sauran a cinye lafiya lau. Sarkin aiki na Lawiza mun gode da kyauta. Ba kyauta ba, ko biyan bashi ya biya mu, to

mun gode na Lawiza mun gode da kyauta. an mata mu rausawa domin gaida Bello. Ina Malam Bello na Lawiza? Mun gode da

kyauta. Ina Malam Haruna? Shi ma dai ya biya mu to mun gode na Tsaiyaba mun gode da

kyauta. Sarkin aiki mu gaida Bello shi ma ya biya mu ba kyauta ba ko biyan bashi ya biya mu to. Mun gode na Lawiza mun gode da kyauta. Baon Kano na Lawiza mun gode da kyauta. Baon Daura na Lawiza mun gode da kyauta. Baon Zango na Lawiza mun gode da kyauta. Baon Yardaje na Lawiza, mun gode da kyauta. Baon Yekuwa Kufai da Hamada na Lawiza mun gode da kyauta.

Mu taka rawarshi wai ko kwa ba mu da lafiya ne? Na Lawiza Malam Bello mun gode da kyauta. Malam Bello Sarkin aiki na Lawiza mun gode da kyauta. Alkawalin amarya da ango ya cika. Mu gaida Haruna na Tsaiyaba mun gode da kyauta. Mu taka rawarshi wai ko kuwa ba mu da lafiya ne? Sai kuwa mu gaida Auwali Abdu za mu gaida Awwali Abdu na Yardaje mun gode da

kyauta. Mu gaida mai gunduma shi za mu gaida na Yardaje mai gunduma mun gode da kyauta.

Mu gaida Guito na Yekuwa shi ma ya biya mu. Na Malam Bello na Lawiza mun gode da kyauta. an masu gari Jamilu shi ma dai ya biya muna. Malam Bello Jamilu to mun gode da kyauta. Malam Bello na Lawiza mun gode da kyauta. Ina Guito na malam Bello? Shi ma mun gode da kyauta. Ba kyauta ba ko biyan bashi ya biya mu. To mun gode na Lawiza mun gode da kyauta. Da karshe ki gaya ma fatan Allah ya kai ka gida lafiya. Malam Bello kuma yana maka godiya. Allah ya saka maka da Alheri. Alla ya maka

Albarka. Allah ya sa ka je gida lafiya. Ka tarda iyalinka lafiya. Allah ya taimaka mu da arziki, Allah ya ba mu abinci, Allah ya ba mu kyaukyawar makoma, Allah ya ba mu cikawa lafiya. Yadda ka zo lafiya. Allah ya maida ka gida lafiya. Alhamdu lillahi. Bayan bayaninki ga sai an kira na Ule ya ara yin roo. Yana wasaka malam Bello. Ya ce a gaya ma Malam Bello wannan Cica mai waa an mutanen Dunawa ne Cica baon Malam Bello na nana Lawizi. A gaya ma Malam Bello wannan Cica an mutanen Dunawa ni da shi da an mota gaba aya. Akwai ni kuma maroin bai Idon Mota na Ule na Mariya El Rando. Muna tare da makaa na ganguna gaba aya rankai. Mutanen Dunawa, na nana Lawiza baban Usmaila baban Ariel na Lawiza sarkin aiki. Cica ne na Dunawa ya wa malam Bello waa da shi da abokanshi. Su Malam Haruna da Kamsila Auwali Abdou su Malam Mansur mutanen Yardaje, da mai gunduma na Yardaje. Babban bao na Lawiza sarkin aiki na Malam Haruna, na Falalu Guito mutumin Jaga mai masaukar bai na Alhaji mai gari Aminu. Na Lawiza sarkin aiki. Baon mutanen daua. Da Zango da Yardaje, da Yekoua ku fai da Hamada. Baon mutanen an Badada da Kwari da Sabuwal Tasha, da Satomawa da Magaria Kitari.

Transcrit par: Tidjani El Dan Bal? Y?koua Editing by Lori DeLucia

................
................

In order to avoid copyright disputes, this page is only a partial summary.

Google Online Preview   Download